Yace kasar Sudan ta kudu zata ninka kokarinta wajen inganta hanyoyin shigar da kayayyakin jin kan al'umma, ya kara da cewa, kasarsa tana fatan kasa da kasa zasu kara azama wajen samar da cigaba da kuma ayyukan jin kai a kasar ta Sudan ta kudu.
Yace babban abin dubawa shine yadda Sudan ta kudun zata samu damammaki wadanda zasu taimaka wajen wanzar da zaman lafiyar al'ummar kasar baki daya, da kuma yadda zasu samu damar zabar shugaban da suke son ya jagorance su ta hanyar karbabbe kuma sahihin zabe.
Yace kasar ta fuskanci dubun dubatar 'yan gudun hijira da wadanda rikici ya raba su da matsugunansu, amma sannu a hankali suna komawa gidajensu bisa radin kansu, hakan ya faru ne sakamakon irin nasarar da aka samu a tattaunawar sulhu da aka bullo da shi a kasar.
Tun a watan Disambar 2013 ne, rikici ya auku a Juba babban birnin Sudan ta kudun, sama da al'ummar kasar miliyan biyu ne rikicin ya daidaita su inda suka tsere makwabtan kasashe domin neman mafaka.