in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An karrama Sinawa masu aikin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu
2017-10-03 13:01:47 cri

Wasu Sinawa dake tallafawa MDD wajen gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya a Juba, babban birnin Sudan ta Kudu sun samu lambar yabo, sakamakon kwazon da suka nuna wajen gudanar da aikinsu a kasar mai fama da tashin hankali.

Bataliyar dakarun kasar Sin ta runduna ta uku dake aikin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu(UNMISS), ta samu lambar yabon ne a yayin wani biki da aka gudanar a ranar Litinin. Wannan ya kasance farin ciki har sau biyu ga Sinawa dake aikin wanzar da zaman lafiyar, bayan da suka gudanar da bikin murnar samun 'yancin kasar Sin a ranar Lahadi.

Jaruman sojin, sun karbi lambobin yabon ne suna sanye da kayan sarki, da takalmansu da farar safar hannu da shudiyar hula dauke da tambarin MDD a lokacin faretin, mataimakin wakilin musamman na sakatare janar na MDD Moustapha Soumare, shi ne ya makalawa dakarun tsaron lambobin yabon.

Soumare ya ce UNMISS, ta nuna yabo bisa irin sadaukarwa da kwazo gami da kwarewar da dakarun na kasar Sin suka nuna ga aikin wanzar da zaman lafiyar.

Ya bayyana cewa 13 daga cikin dakarun tsaron mata ne, a cewarsa wannan ya bayyana a fili irin kwazon da mata ke nunawa wajen aikin wanzar da zaman lafiya.

A cikin shekaru kusan 30 da suka gabata, kasar Sin ta bada gudummawar dakarun kiyaye zaman lafiya ga MDD sama da dubu 30, wadanda suka gudanar da ayyukansu a sassa daban daban na duniya kimanin 24.

A lokacin bikin, an yi shiru na tsawon minti guda, domin girmama dakarun wanzar da zaman lafiyar da suka gamu da ajalinsu a bakin daga a lokacin da suke aikin kiyaye zaman lafiya a Sudan ta Kudun da ma sauran sassa na duniya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China