Hukumar wadda ta bayyana haka a jiya cikin kiyasin al'umma da ta yi na tsakiyar shekara, ta ce a bana, adadin wadanda ke dauke da kwayar cutar kanjamau ya kai kimanin miliyan 7.06.
Kidaddigar ta kuma yi kiyasin cewa, adadin masu dauke da cutar ya kai kashi 18 a tsakanin masu shekaru 15 zuwa 49.
Kasar Afrika ta Kudu ita ce ke da shirin takaita yaduwar cutar mafi girma a duniya wanda ke kula da mutane miliyan 3.4
Fadada shirye-shiryen kiwon lafiya da ke da alaka da kwayar cutar HIV ya taimaka wajen rage asarar rayuka sanadiyyar cututukan da ake iya yadawa da suka hada da tarin fuka da kanjamau.
Domin magance ci gaba da yaduwar cutar, gwamnatin kasar ta kaddamar da wani shiri da ake kira da 90-90-90.
Manufar shirin ita ce, zuwa shekarar 2020, kashi 90 na masu dauke da cutar za su san matsayinsu, sannan kashi 90 na wadanda aka gano suna dauke da ita, za su rika karbar magani.
Har ila yau, gwamnatin na da niyyar tabbatar da cewa, kashi 90 na masu cutar dake karbar magani, sun samu raguwar hayyayafar kwayoyin cutar. (Fa'iza Mustapha)