in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a takaita amfani da ruwa a birnin Cape Town na Afrika ta kudu
2017-09-04 11:38:42 cri
Yayin da ake tsaka da fuskantar fari, an sanar da matakan takaita amfani da ruwa a Birnin Cape Town na kasar Afrika ta Kudu.

Mai rikon mukamin magajin garin Cape Town Patricia de Lille da ta bada sanarwar a jiya, ta ce ba tare da bata lokaci ba, za a dauki wasu matakan takaita amfani da ruwa a birnin.

Ta ce wannan zai kunshi matakin takaitawa na 5 tare da kara matse kaimi wajen kula da hakan.

Za a ci gaba da aiwatar da matakin amfani da lita 87 ga kowane mutum inda gaba daya ruwan da za a yi amfani da shi a kowacce rana zai kasance lita miliyan 500.

Sai dai ta ce a yanzu akwai sabbin matakan kare amfani da ruwa fiye da kima ga kowane iyali inda aka kara matakan ga bangarorin kasuwanci.

Ta ce matakan da ake dauka yanzu na takaita amfani da ruwa zuwa lita miliyan 500, kari ne a kan wadanda aka saba amfani da su domin rage adadin ruwan da ake bukata a kullum, inda ta ce akwai kuma sabbin matakai da gwamnati ke fatan dauka.

Ta kara da cewa matakan wani bangare ne na dabara tsimin ruwa cikin gajere da matsakaicin lokaci. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China