Stephen McGown wanda ke hannun mayakan tun a watan Nuwambar shekarar 2011 a lokacin da suka yi garkuwa da shi yayin da yake yaje hutu Timbuktu na kasar Mali. An damke mutumin ne tare da wani dan kasar Sweden Johan Gustafsson, da wani dan kasar Dutch Hollander Sjaak Rijke..
Dama dai iyalan McGown, da gwamnatin Afrika ta kudu da kasashen duniya sun sha yin kiraye kirayen neman a sake shi.
A yanzu dai an samu nasarar ceto McGown, sashen hulda da kasa da kasa na Afrika ta kudu (DIRCO) ya sanar da hakan.
Mai magana da yawun DIRCO, Brian Dube ya bayyana cewa, suna matukar yin mara da dawowar McGown gida, kuma suna masa fatan samun koshin lafiya da ci gaba da rayuwa a matsayin mutum mai 'yanci a rayuwarsa ta nan gaba.
Gwamnatin kasar Afrika ta kudu ta yi matukar nuna yabo ga wadanda suka taka rawa wajen sakin McGown, musamman gwamnatin kasar Mali da kungiyoyi masu zaman kansu, da daidaikun jama'a. (Ahmad Fagam)