Da yake karin haske kan hakan wakilin mataimakin musamman na shugaban hukumar zartarwar kungiyar tarayyar Afirka mai kula da Somaliya Simon Mulongo ya ce, dangantaka tsakanin AMISON da hukomomin agaji ta taimaka matuka wajen inganta tsarin samar da kayayyakin agajin ga al'ummomin da ke matukar bukata.
Mulongo ya ce sun ji dadin yadda sojoji da hukumomin bayar da agaji ke yin mu'amala, kuma hakan ya taimaka wajen inganta rayuwar al'ummomin dake matukar bukatar kayan agaji a kasar ta Somaliya.
A don haka ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su kara yin cudanya tsakanin sojoji da hukumomin bayar da agaji, don tabbatar da cewa, kayayyakin agaji su kai ga yankuna masu wahalar shiga. (Ibrahim Yaya)