Harvey Schwartz ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana cewa, kamfaninsa yana nuna kyakkyawan makoma ga tattalin arzikin kasar Sin, kasuwar kasar Sin ta samu matsayi mai muhimmanci bisa tsare-tsaren kamfaninsa.
Mista Schwartz ya nuna yabo ga ci gaban tattalin arziki da kasar Sin ta samu, ya ce, saurin bunkasuwar fasahohin sadarwa na zamani na kasar Sin ya fi ta kasar Amurka, ya kan ji mamaki sosai da ganin ci gaban fasahohin sadarwa na zamani da kasar Sin ta samu lokacin da ya kai ziyara a kasar. (Zainab)