in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Birnin Shanghai ya ci gaba a jadawalin birane mafiya bunkasar harkokin hada hadar kudi a duniya
2017-09-11 21:10:01 cri
Bisa labarin da hukumar nazari ta kasar Sin dake birnin Shenzhen ta bayar, an ce, a yau Litinin, bai daya, an fitar da wani jadawali kan alkaluma game da cibiyoyin hada hadar kudi na kasa da kasa karo na 22 a birnin Chengdu na kasar Sin, da birnin Abu Dhabi na kasar tarayyar daulolin Saudiyya. Bisa sabon alkaluman, birnin Shanghai na kasar Sin, ya ci gaba har zuwa matsayi na 6, a yayin da birnin Chengdu, a karo na farko ya shiga jadawalin.

Sakamakon hakan, kawo yanzu, birane 7 na babban yankin kasar Sin, ciki har da Shanghai, da Beijing, da Shenzhen, da Guangzhou, da Qingdao, da Chengdu, da kuma Dalian su ma sun shiga wannan jadawali.

Haka kuma, rahoton ya amince da sakamakon da kasar Sin ta samu, wajen bunkasa cibiyoyin hada hadar kudi. Rahoton yana kuma fatan cibiyoyin hada hadar kudi na kasar Sin, za su kara yin hadin gwiwa da mu'amala da takwarorinsu na sauran kasashen duniya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China