Bisa burin ingiza ci gaban karkara, kasar Sin za ta bunkasa wani ci gaba mafi sauri a bangaren kasuwancin yanar gizo a cikin yankunan karkara da ba su samu ci gaba sosai.
Za a samar da goyon baya ga 'yan kasuwa dake sayar da kayayyakinsu ta internet domin rage kudaden da suke kashewa na tafiyar da harkokinsu, in ji ma'aikatar kasuwancin kasar Sin a ranar Litinin.
Za a kara daukar matakai domin tallafawa da karfafa kwarin gwiwa ga kamfanonin dake kasuwanci ta internet a cikin yankunan karkara, da tsara ayyukan ba da horo ga masu kafa kananan masana'antu, a cewar wata sanarwar da ma'aikatar ta fitar a shafinta na internet.
Dangantaka tsakanin kamfanonin dake kasuwanci ta internet da masu samar da hidima dake kula da masu sayayya a karkara za su samun goyon baya, kuma za a zaminatar da gine ginen dake tallafawa ko suke saukaka kasuwancin internet a cikin yankunan karkara, kana za a ba da kwarin gwiwa ga masu zuba jari domin tallafawa wannan bangare, in ji sanarwar. (Maman Ada)