in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kara mai da hankali kan harkokin kasuwanci
2017-01-05 11:14:45 cri
Kasar Sin za ta kara daukar matakai ta hanyar bullo da sabbin dokoki don saukaka shingayen da ke kawo tarnaki ga harkokin kasuwanci ga masu sha'awar zuba jari a cikin kasar daga ketare.

Firaminista Li Keqiang wanda ya bayyana hakan yayin taron majalisar gudanarwar kasar da ya jagoranta, ya ce nan ba da dadewa ba za bullo da wani tsarin sanya ido a kasuwanni da nufin janyo masu sha'awar zuba jari cikin kasar.

Mr. Li ya ce daga yanzu kananan hukumomin kasar ne za su rika amincewa da wasu dokoki sama da 53, kamar bayar da takardun shaidar bude makarantu masu zaman kansu, da iznin sarrafa auduga, ta yadda za a saukaka batun yiwa harkokin kasuwanci rajista a kasar.

Bugu da kari, a yayin taron majalisar gudanarwar kasar na jiya Laraba, an yanke shawarar cewa, nan ba dadewa ba kasar Sin za ta fito da doka ta farko game da sanya ido a kasuwanni, ta yadda za a rika barin kasuwa ta yi halinta, a wani matakin na kara janyo masu sha'awar zuba jari cikin kasar.

Wannan mataki a cewar mahakuntan kasar ta Sin, za a fara aiwatar da shi a cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 13 wato daga shekarar 2016-2020.

Manufar sabuwar dokar dai, ita ce saukaka harkokin kasuwanci da yin takara da kara samar da kariya ga masu sayan kayayyaki.

Yanzu haka akwai wasu sassa 14 da ke bukatar amincewar majalisar wakilan jama'a kafin su fara aiki kamar yadda doka ta tanada.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China