An bude taron kanana da matsakaitan kamfannonin Sin da kasashen Afrika na shekarar 2016 a birnin Ningbo dake bakin teku a gabashin kasar Sin. Inda aka sanar da cewa, bayan da aka shafe watanni 6 ana shiryawa, yanzu an fara gudanar da shirin hadin gwiwar kanana da matsakaitan kamfannonin Sin da kasashen Afrika a hukunce. Ana saran a cikin shekaru 5 masu zuwa, kanana da matsakaitan kamfannoni 1000 na Sin za su yi hadin gwiwa tare da irin wadannan kamfannoni 1000 na kasashen Afrika.
Cao Fang, mai masaukin baki kana babban sakataren taron kawancen kanana da matsakaitan Sin da kasashen Afrika ya bayyana a gun taron cewa, kanana da matsakaitan kamfannonin Sin suna da kwarewa sosai a fannin na'ura da fasaha, kuma suna da isassun kudade, don haka, za su yi amfani da wadannan fifiko wajen yin hadin gwiwa tare da kamfannonin kasashen Afrika.(Lami)