Masu laifin mambobin wata kungiyar dake kunshe da mutane 32, da suka hada da 'yan Saudiyya 30, da dan Iran guda da kuma dan Afghanistan guda. Biyu daga cikinsu an sallame su, yayin da 15 aka yanke musu hukuncin zaman yari na watanni 6 zuwa shekaru 25.
Yawancin mambobin wannan kungiya suna aiki ne a bangarorin soja da diflomasiyya. An cafke su a shekarar 2013, kafin su bayyana gaban kotu a cikin watan Febrairun da ya gabata.
Kotun ta zarge su da kafa wata kungiya domin samarwa ma'aikatan leken asirin kasar Iran da bayanan soja masu muhimmanci dake shafar Saudiyya, a yayin da kuma wasu mambobin kungiyar suka sami ganawa tare da shugaban juyin juya halin kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
Yawancin wadanda ake zargin sun rike manyan mukamai a bangarorin tattalin arziki, kudi da jami'a, a cewar tashar Al-Arabiya.
Haka kuma hukumonin Riyad sun zargi Teheran da kasancewa mai hannu kan tashe tashen hankali a Gabas ta Tsakiya ta hanyar yin shisshigi a cikin harkokin cikin gida na kasashe kamar Bahrein da kuma Yemen, zargin da Iran kuma ta karyata. Saudiyya ta dakatar da huldar diflomasiyyarta tare da Iran a cikin watan Janairun shekarar da ta gabata tare da kira jakadanta dake kasar ta Iran din. (Maman Ada)