Cikin wata sanarwa da kakakinsa ya fitar a jiya Juma'a, Sakatare Janar din ya ce harin da aka kai wa jami'an a birnin Kidal ka iya zama laifin yaki, inda ya yi kira da a tabbatar da hukunta wadanda ke da hannu.
Antonio Guterres ya kuma jadadda goyon bayan MDD wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya a kasar ta yankin yammacin Afrika, yana mai jajajantawa iyalan wadanda suka mutu tare da yi wa wadanda suka ji rauni fatan samun lafiya cikin gaggawa.
A cewar Shirin wanzar da zaman lafiya na MINUSMA, an farwa sansaninsa dake birnin Kidal a ranar Alhamis da ta gabata, inda aka yi ta harbi da makaman roka, kuma bayanan farko-farko na cewa gomman kwanson bama-bamai iri daban daban ne aka harba sansanin.
Jim kadan bayan nan ne kuma, aka farwa jami'ai dake wajen sansanin, al'amarin da ya yi sanadin raunatar 8 daga cikinsu. (Fa'iza Mustapha)