in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta jawo hankalin duniya sosai a fannin sha'anin kera kayayyakin zamani
2017-02-13 10:36:07 cri
Jaridar The New York Times ta kasar Amurka ta ba da labari a kwanakin baya cewa, kamfanin Global Foundries na kasar Amurka ya sanar da zuba jari na dala kimanin biliyan 10 a kasar Sin, wannan ya shaida cewa, Sin ta jawo hankalin duniya sosai a fannin kera kayayyakin zamani.

Rahotanni na cewa, koda yake gwamnatin kasar Amurka karkashin jagaroncin Trump ta matsawa kamfanin Intel da kamfanin Foxconn da sauran kamfanonin fasahohin zamani lamba, lamarin da ya sa suka sanar da kafa masana'antu a kasar Amurka a kwanakin baya, amma kamfanin Global Foundries ya bayyana shirinsa na zuba jari, wannan ya bayyana cewa, hankalin wasu kamfanoni na ci ga da karkata ga kasar Sin.

Bugu da kari, kamfanin na Global Foundries zai kafa sabon reshensa na kera kayayyakin zamani a birnin Chengdu na kasar Sin, wannan sabon misali ne da babban kamfanin duniya ya yi na zuba jari a kasar Sin bisa goyon baya daga gwamnatin kasar Sin.

Aikin gina masana'antar kera na'ura da ake kira 'wafer' a Turance a birnin Chengdu na kasar Sin shi ne wani aikin da ya shafi mafi yawan fasahar zamani a duniya da kamfanin Global Foundries ya yi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China