in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin kasar Sin ya bayyana ra'yoyi uku game da yadda za a gudanar da aikin 'yan gudun hijira
2017-10-05 12:43:37 cri

Ma Zhaoxu, zaunannen wakilin kasar Sin da ke Majalisar Dinkin Duniya ya ba da jawabi a yayin muhawarar da kwamitin kula da 'yan gudun hijira na majalisar ya yi a jiya Laraba, inda ya bayyana matsayin kasar Sin kan batun 'yan gudun hijira.

Ma Zhaoxu na ganin cewa, bisa kokarin da kasashen duniya suka yi, yanzu akwai muhimmiyar dama game da yadda za a kula da batun 'yan gudun hijira. Ra'ayoyin kasar Sin kan wannan batun su ne, na farko, ya kamata a kara mara baya ga hukumar kula da 'yan gudn hujira ta MDD ta UNHCR da kasashen dake karbar 'yan gudun hijira, a waje daya kuma ya kamata a yi kokarin warware matsalolin rashin kwanciyar hankali da rashin daidaiton ci gaba, da kawo karshen rikice-rikice ta hanyar tattaunawa, da kara tallafawa kasashe masu tasowa, ta yadda 'yan gudun hijirar za su koma kasashensu ba tare da wata matsala ba, da sa kaimi ga ci gaban kasashensu yadda ya kamata.

Na biyu kuma shi ne, kasashen duniya su kara yin hadin gwiwa. Yanzu ana gwajin Tsarin mayar da 'yan gudun hijira gida a wasu kasashe, ya kamata hukumar UNHCR ta koyi wasu fasahohi daga wannan aikin, a kokarin samar da bayanai masu amfani ga aikin tsara yarjejeniya kan batun 'yan gudun hijira ta duniya.

Ra'ayi na uku shi ne, yayin da kasashen duniya ke daidaita batun 'yan gudun hijira, ya kamata a magance tsoma baki a harkokin cikin gida na kasashen da abin ya shafa, kana bai kamata a sanya siyasa ko fakewa da tsarin kiyaye 'yan gudun hijira na duniya a cimma wata bukata ba.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China