in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare janar na MDD ya yi kira ga kasashen da suka ci gaba su ba 'yan gudun hijira mafaka
2017-06-21 10:00:33 cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kira ga kasashen da suka ci gaba, su ba karin 'yan gudun hijira mafaka, sannan su raba nauyin da kasashe masu tasowa dake karbar kashi 80 bisa dari na 'yan gudun hijira a duniya.

Guterres ya nemi kasashen da suka ci gaba su kara karbar 'yan gudun hijira, ta yadda za a kai a kalla matakin da ake shekaru 2 zuwa 3 da suka gabata, domin a samu a raba nauyin da kasashe masu tasowa dake karbar miliyoyin 'yan gudun hijira.

A jiya Talata ne aka gudanar da ranar 'yan gudun hijira ta duniya, kuma a daidai lokacin da ake rufe iyakokin a fadin duiniya, ake kuma watsi da 'yan gudun hijira, Antonio Guterres ya tunatar da kasashen duniya cewa, kare 'yan gudun hijira ba marawa juna baya ko tallafi ba ne, abu ne da ya zama dole karkashin dokar kasa da kasa.

A don haka, ya yi kira ga kasashe mambobin majalisar kada su rufewa 'yan gudun hijira dake neman mafaka kofa, sannan kuma su kare iyakokinsu ta hanyar da ta dace. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China