in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya yi bayani kan batun 'yan gudun hijirar Gabas ta Tsakiya
2017-06-24 13:56:40 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, da hadin gwiwar takwaransa na kasar Lebanon sun gana da 'yan jarida jiya a birnin Beirut na Lebanon, inda ya yi bayani kan manufar kasar Sin game da batun 'yan gudun hijirar Gabas ta Tsakiya.

Wang Yi, ya ce ya kamata a gaggauta warware matsalar kasar Syria a siyasance, domin ba 'yan gudun hijira damar komawa gidajensu.

Ya kara da cewa, idan har ana son warware batun 'yan gudun hijira daga tushe, to ya kamata a dukufa wajen kyautata zaman rayuwarsu tare da kawar da talauci a tsakaninsu.

Har ila yau, Ministan ya ce kasar Sin, ta na son dukufa tare da gamayyar kasa da kasa, wajen warware matsalolin dake daukar hankalin al'ummomin kasa da kasa, da kuma ba da taimako ga 'yan gudun hijira wajen warware matsalolin da suke fuskanta, ta yadda za su samu damar komawa kasarsu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China