Wu Haitao ya ce Hanyoyin da suka fi dacewa wajen warware matsalar sun hada da, cimma zaman lafiya da kwanciyar hankali, da tabbatar da samun bunkasa tare, da karfafa hadin kai tsakanin kasa da kasa, da kuma kyautata matakan gudanar da harkokin duniya.
Wakilin na Sin ya bayyana haka ne a jiya, yayin taro kan batun 'yan gudun hijira da bakin haure na Bahar Rum da aka shirya a wani bangare a babban taron MDD karo na 71.
Ya kara da cewa, kamata ya yi kasashen dake da 'yan gudun hijira da wadanda jama'arsu ke fita ci rani, da wadanda suke ratsawa ta cikinsu da kuma wadanda 'yan ci ranin da 'yan gudun hijira ke burin zuwa, su hada hannu tare da daukar nauyin dake kansu, ta yadda kasashen da al'amarin ya shafa za su bude kofofinsu ga 'yan gudun hijira da bakin haure ba tare da nuna musu bambanci ko watsi da su ba.
Mista Wu ya kara da cewa, kasar Sin ta dauki batun warware matsalolin 'yan gudun hijira da bakin haure da muhimmanci, ta na kuma kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali na duniya, tare kuma da tsayawa kan goyon bayan kasashe masu tasowa wajen cimma burin samun ci gaba, da kara himmantuwa wajen samar da tallafin jin kai ga wasu kasashe da hukomimin duniya da suke da bukata.
Ya zuwa yanzu dai, kasar Sin ta samar da kayayyaki da kudi da darajarsu ta wuce RMB miliyan 680 ga kasar Syria, sannan a watan Janairun da ya gabata, ta tsaida kudurin kara ba ta taimakon RMB miliyan 200.
A Kwanankin baya, kasar Sin ta kara samar da tallafin kudi na dalar Amurka miliyan 1 ga hukumar lafiya ta duniya WHO da asusun tallafawa kananan yara UNICEF da kuma UNHCR mai kula da yan gudun hijra na MDD, domin karfafa masu gwaiwar ba da tallafin jin kai ga 'yan gudun hijira. (Bilkisu)