Daga cikin mutane 302 dake cikin jiragen 2, an samu damar ceto 57, yayin da wasu daga cikin ragowar 245 suka mutu ko bata.
Cecile Pouilly wadda ta bayyana haka a jiya, ta ce a daren ranar 5 ga wata, wani jirgin ruwa mai dauke da 'yan gudun hijira 132 ya nutse a yankin tekun Bahar Rum, inda aka ceto 50 daga cikin mutanen tare da kai su tsibirin Sicilia na kasar Italiya. Sai dai, ana fargabar ragowar 82 da suka hada da 'yan mata da yara, sun riga sun mutu.
Har ila yau, ta ce a ranar 7 ga wata, wani jirgin ruwa mai dauke da 'yan gudun hijira 170 ya nutse a yankin tekun dake dab da kasar Libya, inda ake tsammanin 163 daga cikin mutanen sun mutu ko sun bata a cikin teku.
Alkaluman da hukumar UNHCR ta fitar sun bayyana cewa, kimanin 'yan gudun hijira dubu 20 ne suka tafi kasar Italiya ta Bahar Rum a bana, inda 520 daga cikin su suka mutu a kan hanya.(Bello Wang)