Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, UNHCR ta ce yaki da rikice-rikice da ake fuskanta a fadin duniya na kara raba mutane da muhallansu bisa tilas.
Cikin rahotonta na shekara-shekara kan halin da 'yan gudun hijira ke ciki a duniya, wanda ta fitar jiya a Geneva, hukumar ta ce zuwa karshen 2016 akwai mutane da suka tserewa matsugunansu bisa tilas kimanin miliyan 65.6, kuma 300,000 daga ciki sun kai sama da shekara da tserewa.
A cewar shugaban hukumar Filippo Grandi, babu yadda za a yi a taba amincewa da wannan adadi, yana mai cewa, adadin na kira ne da babbar murya, ga bukatar mara baya ga juna da mai da hankali wajen warware rikice-rikice da kare aukuwarsu.
Daga cikin mutanen miliyan 65.6, miliyan 22.5 'yan gudun hijira ne, adadin da ba a taba gani ba a baya.
A cewar rahoton, rikicin da ake a Syria, shi ne ya fi ko ina a duniya samar da 'yan gudun hijira, inda al'ummar kasar kimanin miliyan 5.5 ke zaune a wajen kasarsu. (Fa'iza Mustapha)