in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta ci bashin dala miliyan 125 don yaki da cutar shan inna
2016-08-26 09:53:53 cri

Ministan lafiya a Tarayyar Najeriya Isaac Adewole, ya ce bankin duniya ya baiwa Najeriya rancen kudi har dalar Amurka miliyan 125, domin yaki da cutar shan inna ko polio, tare da sauran matsalolin lafiya da ake fama da su a kasar. Mr. Adewole ya bayyana hakan ne, yayin da yake yiwa kwamitin lafiya a matakin farko na majalissar dattijan kasar bayani game da wasu batutuwa da suka shafi ayyukan ma'aikatar sa.

Ministan ya ce bisa amincewar majalissar, za a kashe dala miliyan 60 wajen yaki da cutar polio, kana za a kashe sauran dala miliyan 65 wajen sayen alluran rigakafi. Ya ce sakamakon bullar cutar da aka samu a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar, an yiwa yara kanana 'yan kasa da shekaru 5 su kimanin 800,000 rigakafin cutar a kananan hukumomi 5 dake jihar.

Adewole ya ce ma'aikatar sa na fatan yin hadin gwiwa da sauran masu ruwa da tsaki, wajen tabbatar da an kakkabe cutar daga dukkanin sassan kasar, da ma makwaftanta, ta hanyar gudanar da zagaye 6 na rigakafi ga kananan yara.

A ranar 11 ga watan Agustan nan ne aka samu rahoton sake bullar cutar shan inna a jihar Borno. Gabanin hakan a shekarar 2012, Najeriya ta taba zama kan gaba a kasashen da ke fama da wannan cuta, inda kusan rabin masu dauke da ita ke zaune a sassan kasar daban daban. Sai dai kuma kwazon da gwamnatin kasar ke yi wajen yaki da ita a 'yan shekarun nan, ya bada damar cimma gagarumar nasarar dakile yaduwar ta.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China