Kungiyar masu kiwon kaji ta Najeriya PAN, ta fada cewa a makon da ya gabata wasu gidajen gona 6 a jihar Plateau dake tsakiyar Najeriya sun tafka hasarar kaji a kalla dubu 11, sakamakon bullar cutar murar tsuntsaye.
Wannan matsala ta yi matukar jefa manoman jihar Plateau cikin rudani, tun bayan samun rahoto game da bullar cutar a makon jiya.
Cutar murar tsuntsayen wacce ke saurin yaduwa tana iya cutar da tsuntsaye har ma da bil Adama.
Barkewar wannan annobar tana matukar haifar da babbar illa wajen hasarar kudaden shigar masu kiwon kaji, kana tana yin illa ga lafiyar mutane dake amfani da kajin da ake kiwatawa.
Sanarwar ta danganta matsalar saurin yaduwar cutar da cewa laifin masu kiwon kajin ne, saboda kin kaiwa rahoton bullar cutar a kan lokaci ga hukumomin da abin ya shafa.
Shugaban masu kiwon kaji na jihar Plateau John Dasar, ya ce a shekarun 2015 da 2016 masu kiwon kaji 130 ne suka tafka hasara, amma har yanzu ba su samu wani tallafi daga wajen hukuma ba.(Ahmad Fagam)