in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta kaddamar da rigakafin cutar zazzabin shawara a kasashen Afirka
2016-08-17 10:43:16 cri
Mai Magana da yawun MDD yace an fara gudanar da allurar riga kafin cutar zazzabin shawara mafi girma a kasashen Angola da jamhuriyar demokaradiyyar Kongo a wannan mako.

Hukumar lafiya ta duniya WHO, tare da hadin gwiwar hukumomin agaji na kasa da kasa ne suke gudanar da rigakafin domin dakile yaduwar annobar zazzabin shawara wanda ya barke, ya hallaka rayukan sama da mutane 400, sannan wasu dubbai suka jikkata.

Mataimakin mai Magana da yawun MDD Frahan Haq, ya fada a taron manema labaru cewar, cutar zazzabin shawaara ta bazu ne a manyan garuruwa dake da cunkoson jama'a, da wasu birane, kana tana kokarin tsallakawa zuwa makwabtan kasashe, don haka ya zama dole a gudanar da riga kafin dakile yaduwar cutar.

Ya ce tuni aka samar da alluran riga kafin zazzabin shawarar ga mutane sama da miliyan 13 a kasar Angola, da kuma mutane miliyan 3 a demokaradiyyar Kongo.

Sai dai a cewarsa, har yanzu akwai yankuna da ake fargabar yiwuwar fuskantar cutar, don haka an shirya gudanar da riga kafin a babban birnin DRC Kinshasa, da kuma kan iyakar kasar da Angola dake da tazarar kilomita 2,600.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China