Ma'aikatar lafiya ta kasar Uganda ta shelanta kawo karshen cutar zazzabin shawara wadda ta hallaka mutane 3, sannan wasu mutune 7 suke kamu da kwayoyin cutar a shiyyar tsakiya da yammacin kasar.
Anthony Mbonye, shi ne mai rikon daraktan sashen lafiya na kasar, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, kasar ta ayyana kawo karshen cutar ne kasancewar babu wata alama dake nuna an sake samun rahoton yaduwar cutar a kasar daga ranar 1 zuwa 30 ga watan Yuni.
Mbonye ya ce, "A yau Talata, ina sanar da dukkan al'umma da kungiyoyin yaki da cutar zazzabin shawara na shekarar 2016 cewar, an yi nasarar dakile yaduwar cutar kacokan".
Daga ranar 24 ga watan Maris zuwa 4 ga watan Mayun wannan shekara, aka samu rahoton bullar annobar zazzabin shawara a kasar Uganda, yawan mutanen da suka kamu da cutar ya kai 65 a yankunan Masaka da Kalangala dake gundumar tsakiyar kasar, sai kuma yankin Rukungiri dake gundumar yammacin kasar.(Ahmad Fagam)