in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taro kan ciwon kansa karo na 10 na AU ya yi kiran karfafa yaki kan cutar
2016-07-28 10:44:09 cri

Taro karo na 10 kan ciwon kansa na kungiyar tarayyar Afrika AU da ya gudana daga ranar 24 zuwa 27 ga watan Yuli a birnin Addis Abeba na kasar Habasha, ya yi kiran da a kara karfafa kokari wajen yaki da kansa daga dukkan fannoni, musammun ma ciwon kansan dake shafar farjin mata, nono da kuma mazakuta.

Taron ya sake yin kira tare da mayar da hankali sosai game da karuwar matsalolin dake da nasaba da ciwon kansan dake shafar farjin mata, nono da kuma mazakuta a Afrika.

A nahiyar Afrika, hadarin gyanbon farjin mata, nono da kuma mazakuta na karuwa cikin sauri a wasu yankunan nahiyar Afrika, in ji taron.

Haka kuma mahalarta taron sun yi la'akari da karancin zuba jari a cikin gine gine domin yin rigakafi, gano cutar cikin sauri, ba da jinya da makamantan haka.

Wata sanarwar da aka fitar bayan taron ta jaddada kan aikin fadakar da kan jama'a tare da halartar dukkan bangarori masu ruwa da tsaki, har ma da shugabannin addinai da wakilan al'umomi, kungiyoyin fararen hula da kafofin watsa labarai.

Haka kuma, sanarwar ta yi kira kan yin amfani da bunkasa kimiyya domin ingiza ci gaban gano ciwon kansa, bincike, ba da jinya da makamantan haka. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China