in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Burundi ta zargi EU da neman dagula al'amura a kasar
2017-06-06 09:48:43 cri
Mahukuntan kasar Burundi sun zargi kungiyar tarayyar Turai (EU) da neman tayar da zaune tsaye a cikin kasarta. Wannan na zuwa ne, bayan da gwamnatin Burundin ta ce ta bankado wasu muhimman takardu dake nuna hannun kungiyar damu-damu a kokarin wargaza kasar.

Kakakin gwamnatin Burundi Philippe Nzobonariba ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, muhimman takardun, da wasu gamsassun bayanai marasa dadin ji sun nuna tsoma hannun tawagar kungiyar ta EU da suka ziyarci kasar a shekarar 2014, watanni da dama kafin tashin hankalin da ya barke a cikin kasar da kuma juyin mulkin kasar na shekarar 2015 da bai yi nasara ba

Nzobonariba ya kara da cewa, muhimman bayanai sun kuma nuna cewa, kungiyar ta dauki nauyin wasu mutane da kungiyoyi domin su wargaza kasar, wadanda a halin yanzu ma'aikatar shari'ar kasar ta mika sammacin kasa da kasa domin a damke su.

A cewarsa, wadannan muhimman bayanai da sauran hujjoji, su ne suka tilasta wa mahukuntan kasar sanar da cewa, akwai hannun ketare a yunkurin yiwa zaben kasar na shekarar 2015 zagon kasa.

A saboda haka ya ce, muhimman takardun da ka gano, sun tabbatar da cewa, wasu bangarori kamar kungiyar tarayyar Turai sun taka muhimmiyar rawa wajen ganin an kifar da gwamnati a kasar Burundi.

A watan Maris din shekarar 2016 ne kungiyar ta EU ta yanke shawarar dakatar da baiwa kasar ta Burundi tallafi, bisa korafin cewa, gwamnatin Burundi ta gaza wajen daukar matakan da suka dace na magance matsalar take hakkin bil-Adama, da shirye-shiryen mika mulki da kuma yadda ake mutunta dokoki. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China