in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'yan kasar Sudan ta kudu 240 sun samu tallafin karatu a jami'o'in kasar Sin
2017-08-27 13:01:34 cri
Gwamnatin kasar Sin ta bada tallafin karatu ga daliban kasar Sudan akalla 240, domin karatun digiri da digiri na biyu a jami'o'i daban-daban na kasar.

Mukaddashin jakadan kasar Sin a Sudan ta Kudu Li Xiangfeng, ya ce an bada tallafin ne a bangarori da dama da suka hada da na kiwon lafiya da tsimi da tanadi da aikin gona da harkokin kasashen waje.

Jami'in ya ce shirin wani bangare ne na gudunmuwar kasar Sin ga Sudan ta Kudu ta hanyar mara mata baya wajen raya tattalin arziki da rayuwar al'umma.

A nasa bangaren, Ministan kula da ilimi a manyan makarantu na Sudan ta Kudu Yien Oral Lam, ya godewa Gwamnatin kasar Sin bisa sha'awar da ta nuna na tallafawa kasar, ya na mai cewa, Sudan ta kudu za ta ci gaba da hada hannu da al'ummar kasar Sin saboda kudurin da suke da shi na taimakawa al'ummar kasar.

Shi kuwa wakilin kungiyar aminci tsakanin Sudan ta kudu da kasar Sin Luka Monoja, ya ce tallafin zai karfafawa al'ummomin kasashen gwiwar mu'amala da juna tare da bunkasa huldar dake tsakanin Gwamnatocin biyu.

Ya kuma bukaci daliban su yi amfani da damar wajen sanin tarihin yadda kasar Sin ta sauya daga kasa mai tasowa zuwa kasa mafi karfin tattalin arziki na 2 a duniya, ta yadda za su yi amfani da shi wajen samar da ci gaba ga kasar ta gabashin Afrika da yaki ya daidaita . (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China