A cewar sashen dake lura da harkokin cikin gida da lalitar Amurka, takunkumin ya shafi mataimakin ministan tsaron kasar Malek Reuben, da ministan watsa labaran kasar Michael Makuei, da tsohon hafsan hafsoshin sojojin kasar Paul Malong.
Wata sanarwa da sashen lura da latitar Amurkan ya fitar ta bayyana cewa, kamfanoni 3 da lamarin ya shafa mallakar Mr. Reuben ne, kuma Amurka za ta ci gaba da jaddadawa jagororin Sudan ta kudu, wajibcin biyayya ga yarjejeniyar tsagaita wuta.
Kaza lika ya zama tilas a martaba yarjejeniyar shekarar 2015 da aka sabunta, wadda ta tanaji matakan warware takaddamar siyasa dake addabar Sudan ta kudu, ta hanyar tattaunawa mai ma'ana tare da tsagin 'yan adawar kasar. (Saminu)