in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta Kudu ta yi sammacin jakadan Amurka a kasarta game da wasu takunkumai
2017-09-12 11:36:32 cri
Sudan ta Kudu ta aike da sammaci ga mukaddashin Jakadan Amurka a kasar jiya Litinin, domin nuna adawa da takunkuman da aka sanyawa wasu jami'anta 3 da suka kunshi tsoffi da wadanda ke bakin aiki. Mataimakin Sakataren ma'aikatar harkokin wajen kasar Bal Valentino Akol, ya ce sun gana a birnin Juba da Micheal Morrow, domin sanin dalilan da suka sanya aka kakaba takunkuman da ya kira na rashin adalci, la'akari da cewa ba a hada da bangaren adawa dake dauke da makamai ba.

A ranar 6 ga watan Satumba ne baitul malin Amurka ta kakaba takunkumai da haramcin tafiya wanda ya hada da rufe asusun ministan yada labaran kasar Micheal Makuei da mataimakin babban hafsan sojin kasar Reuben Malak da kuma tsohon babban hafsan sojin Paul Malong. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China