Kakakin kungiyar a Sudan ta Kudu Mari Aftret Morvert, ta ce sun dakatar da ayyuka na wucin gadi a Equatoria domin nazarin yanayin tsaro a yankin tare da makokin abokin aikinsu.
Mari Mortvert ta kara da cewa, kungiyar na gudanar da bincike kan mutuwar Direban nata kafin ta fito ta bayyana matsayarta game da aiki a yankin.
An kashe Lukudu Kennedy Laki Emmanuel wanda ya fara aiki da kungiyar a matsayin direba a shekarar 2014 ne, bayan wasu tsageru da ba a san ko su waye ba, sun yi harbi kan jerin gwanon motocin kungiyar. (Fa'iza Mustapha)