in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya kaddamar da shirin tada komadar tattalin arziki
2017-04-06 10:12:27 cri

A jiya Laraba ne shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya bayyana cewa, gwamnatin kasar ta kama hanyar da ta dace wadda za ta zama waraka wajen tada komadar tattalin arzikin da kasar ta tsinci kanta a halin yanzu, a lokacin da shugaban kasar ya kaddamar da wani shiri na musamman na farfado da tattalin arziki, da samar da ci gaba wato ERGP a takaice.

Shugaban Buhari ya ce, shirin farfado da tattalin arzikin kasar da samar da ci gaba zai tattaro dukkan bangarori da suka hada da aikin gona, da samar da abinci, makamashi da sufuri da ababan more rayuwa, masana'antu da zuba jari, dukkaninsu cikin wani daftari guda.

Bayani mai kunshe da shafuka 140, an shirya shi ne musamman domin tsame kasar daga halin matsin tattalin arziki da take ciki, da kuma shirin dogon zango, wanda tattalin arzikin kasar zai ci gaba da samun bunkasuwa.

Shirin wanda aka kaddamar da shi a fadar shugaban kasar dake Abuja, ana sa ran shirin zai samar da ci gaba cikin sauri wajen samun farfadowa da ci gaban kayayyakin more rayuwa.

Sabon shirin tattalin arzikin kasar zai kuma farfado da dawwamamman ci gaba, da samun bunkasuwa, da zuba jari don ci gaban al'umma, da kuma samar da tasiri na yin gogayyar ci gaban tattalin arziki a duniya.

Shugaban Buhari ya ce, sabon shirin zai habaka ci gaban tattalin arzikin kasar da kashi 7 cikin 100 nan da shekarar 2020, ya kara da cewa, kasar za ta dogara da masana'antun cikin gida maimakon dogaro kan shigo da kayayyaki daga kasashen ketare.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China