Najeriya ta shiga aikin maido da kudaden kasar aka sace dake cikin bankunan kasashen waje domin ingiza tattalin arziki, in ji ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama a ranar Alhamis.
A yayin wani taron manema labarai a birnin Abuja, bayan halartarsa a babban taron MDD, mista Onyeama ya tabbatar da cewa, gwamnati ta riga ta tantance wasu kasashe, inda aka boye kudaden Nijariya, kuma tana aiki kafa da kafa tare da wadannan kasashe.
Najeriya ta tuntubi yawancin kasashe, inda aka ajiye kudadenta da aka sace domin neman a maido mata da su, in ji ministan.
A cewarsa, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tarurruka tare da shugabannin kasashe da dama, da suka hada da shugaban Amurka Barack Obama, da kuma faraministar Burtaniya Theresa May, kan batun maido wa Najeriya kudadenta da aka sace, da sauransu.
Ministan harkokin wajen Najeriya ya bayyana wa 'yan jarida cewa, shugabannin duniya sun dauki niyyar ta tabbatar da cewa, za su maido wa Najeriya wadannan kudaden da aka sace cikin sauri. (Maman Ada)