in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya na cike da fatan alheri kan makomar samun bunkasuwa duk da koma bayan tattalin arziki
2016-09-28 10:04:39 cri

Duk da matsalolin dake nasaba da jerin koma bayan tattalin arziki, tattalin arzikin Najeriya na cike da makoma mai haske, in ji ministan sadarwa da al'adun kasar, Lai Mohammed.

Ministan ya yi wadannan kalamai masu kwantar da hankali a yayin bukukuwan ranar yawon bude ta kasa da kasa ta shekarar 2016 a Eko Atlantic City dake birnin Lagos.

Wannan birnin na miliyoyin dalar Amurka, an gina shi baki dayansa ta hanyar zuba jarin masu zaman kansu, bisa tabo da rairayi da aka rika kwasowa daga tekun Atlantic, hakan ma wata shaida ce ta makoma mai haske, in ji mista Mohammed.

Jami'in ya yi kira ga masu zuba jari da su ba da taimako wajen kawo sauyi ga yankunan yawon bude ido da dama na kasar a matsayin wasu wuraren janyo hankalin masu yawon shakatawa, tare da bayyana cewa, Najeriya ta tanadi wurare da dama na yawon bude ido daga indallahi da kuma wadanda 'dan adam ya gina.

Gwamnatin za ta taimaka ga kara zuba jari mai yawan gaske wajen bunkasa ababen more rayuwa domin kara baiwa kowa damar zuwa wuraren yawon bude ido, in ji mista Mohammed. Ya jaddada cewa, yawon bude ido da kirkire kirkire sun kasance wani "sabon man fetur" na tsarin fadada tattalin arzikin Najeriya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China