Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar, matsin tattalin arzikin da kasar ke fuskanta a halin yanzu ya faru ne sakamakon rashin jagoranci na gari da gwamnatocin baya suka tafka a shekaru da dama da suka gabata a kasar, wacce ke yammacin Afrika.
A wata sanarwa da aka baiwa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua a jiya Talata, Buhari ya ce, gwamnatinsa za ta yi iyakar kokarinta wajen yin garambawul ga sha'anin tattalin arzikin kasar.
Shugaban na Najeriya ya kara da cewar, halin rikicewar tattalin arzikin da kasar ta shiga, daya ne daga cikin kura kuran da kasar ta tafka wajen dogaro da hanya daya tilo wajen samun kudaden shigarta, ya kara da cewar, gwamnatocin baya ba su yi tattalin makudan kudaden da kasar ta samu na cinikin man da ta yi ba.
Buhari ya ce, daga cikin dabarun da gwamnatinsa ta bullo da shi wajen aza kasar kan kyakkyawar makoma shi ne daidaita tattalin arzikin kasar ta hanyar kasafin kudin kasar na shekarar 2016, wanda ya fi mai da hankali wajen rage shigo da kayayyaki daga kasashen waje, da kuma mai da hankali wajen fitar da kayayyaki kasashen waje, da inganta masana'antu, musamman wajen samar da kayayyakin da masana'antu ke bukata, da samar da ayyukan yi, da samar da dabarun bunkasa harkokin kasuwanci, da janyo hankalin masu zuba jari zuwa kasar.(Ahmad Fagam)