Ministar kula da al'amurran mata da walwalar jama'a ta Najeriya Aisha Jummai Alhassan ta ce, gwamnatin kasar na ci gaba da daukar kwararan matakai domin dakile matsalar rikicin tattalin arziki da kasar ke fuskanta.
Da take jawabi a lokacin taron jama'a a jihar Kano dake arewa maso yammacin kasar, Aisha Jummai Alhassan, ta bayyana cewa, gwamnatin kasar mai ci tana daukar dukkannin matakan da suka dace domin kawar da halin matsi da al'ummar kasar ke fuskanta a sanadiyyar tabarbarewar tattalin arziki dake damun kasar.
An dai shirya taron ne da nufin wayar da kan al'umma game da halin matsin tattalin arzikin da kasar ke fuskanta, da kuma hanyoyin da za'a bi wajen tunkarar matsalar.
A wani labarin kuma, cibiyar bunkasa kasuwanci da masana'antu ta jihar Legas (LCCI), ta yi hasashen cewa, Najeriya za ta cimma nasarar fita daga halin matsin tattalin arziki a shekarar 2017 mai zuwa.
Shugaban LCCI, Nike Akande, ya bayyana cewa, kasancewar Najeriyar ce kasa mafi girma a nahiyar Afrika, kasar ba za ta dauki dogon lokaci ba wajen koma hayyacinta, kana za ta ci gaba da rike matsayinta na kasa mafi karfin tattalin arziki cikin kungiyar kasashe renon Ingila.
Shi ma manajan daraktan bankin raya ci gaban masana'antu na Najertiyar (BOI), Waheed Olagunju, ya bayyana cewa, matakin da kasar ta dauka na zuba jari da kuma sauya akalar hanyoyin samun kudaden shigarta za su fitar da kasar daga cikin halin matsin tattalin arziki cikin gajeren lokaci.(Ahmad Fagam)