in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya ta tusa keyar wasu bakin haure zuwa kasashensu
2017-09-13 14:01:47 cri
A jiya Talata ne, hukumar kula da bakin haure ta kasar Libya ta tusa keyar wasu bakin haure da suka shiga kasar ba bisa doka ba, wadanda suke zauna a wata cibiyar tsugunar da bakin haure dake birnin Tripoli na kasar zuwa kasashensu

Kakakin hukumar ya bayyana cewa, mutanen da aka mayar gida a wannan karo sun hada da bakin haure 53 daga kasar Nijeriya da kuma wasu 24 daga kasar Bangladesh, wadanda suke yunkurin zuwa nahiyar Turai, amma jirgin ruwan da suke ciki ya gamu da matsala a kan teku, inda ma'aikatan tsaron gabar teku ta kasar Libya ta gano su. Kakakin ya bayyana cewa, hukumar kula da bakin haure ta kasa da kasa ta samar da taimako da goyon baya ga aikin mayar da bakin haure kasashensu da kasar Libya ta yi.

Tun a shekarar 2011 ne, kasar Libya ta gamu da matsalar tsaro,lamarin da ya sa gwamnatin kasar sa ido sosai kan iyakar kasar ta gabar teku. Bakin haure sun maida kasar Libya a matsayin wurin da suke yada zango, inda suke ratsa bahar Rum a kan hanyarsu ta zuwa kasashen Turai. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China