in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin Sulhu ya tsawaita shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a Libya
2017-09-15 11:17:24 cri
Kwamitin Sulhu na MDD ya yanke shawarar tsawaita shirin wanzar da zaman lafiya na (UNSMIL) a Libya har tsawon shekara guda, wato zuwa ranar 15 ga watan Satumbar 2018.

Daukacin mambobin majalisar ne suka amince da kudurin mai lamba 2376, wanda ya tsawaita ayyukan shirin, tare da mara baya ga tsarin siyasar da ke kunshe cikin yarjejeniyar siyasar kasar da aka cimma.

Manyan ayyukan shirin sun hada da mara baya ga muhimman cibiyoyin kasar da samar da ayyukan jin kai idan ana bukata tare da sa ido kan hakkokin dan Adam da bada rahoto.

Sauran sun hada da kawar da makamai da sauran abubuwa dake da alaka da yaki da yaduwar makamai da kuma taimakawa gwamnatin kasar a kokarin da take na farfado da yankunan da rikici ya rutsa da su, ciki har da wadanda aka 'yanto daga hannun kungiyar IS. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China