in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a kaddamar da sabon littafi game da layin dogon da kasar Sin ta gina tsakanin Mombasa zuwa Nairobi
2017-09-29 10:31:41 cri
Nan ba da dadewa ba za a wallafa wani littafi, wanda a cikinsa 'yan kasar Kenya da Sinawa da suka yi aikin gina layin dogon nan da kamfanin kasar Sin ya gina tsakanin Mombasa zuwa Nairobin kasar Kenya, za su bayyana labaransu game da yadda wannan aiki ya gudana da ma tarin nasarorin da aka kai ga cimma a wannan zango

A jiya Alhamis ne kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin da kamfanin nan da ya shahara a fannin al'adu da nishadantarwa mai suna "Enjoy Culture & Media" suka sanya hannu kan yarjejeniyar wallafa wannan littafi mai suna "My Railway, My Story" wanda aka tsara shi ta hanyar bayyana labaran yadda aikin gina layin dogon ya gudana.

Za a fassara littafin ne daga shirin talabijin din nan mituna 90 da tun farko aka tsara game da wannan aiki zuwa harsunan Sinanci da Turancin Ingilishi da kuma Faransanci, wanda ke bayyana gwagwarmayar da 'yan asalin Kenya da Sinawan da suka yi aikin gina wannan hanya suka fuskanta yayin wannan aikin da ya kasance mafi girma tun samun 'yancin kasar ta Kenya.

Ya zuwa yanzu dai an watsa wannan shiri da aka kasa shi gida uku, wanda tun farko aka shirya cikin harshen Ingilishi daga bisani kuma aka fassara shi zuwa harsunan Sinanci da Faransanci da Swahili, a gidajen talabijin na kasashen Sin da Najeriya da kuma Zambia, kana ana iya samunsa a shafin intanet da sauran kafofin sada zumunta. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China