Kakakin hukumar Wilson Uwajaren, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya cewa, an kama jami'an ne bayan sun ki amsa gayyatar da hukumar ta yi musu a baya don amsa tambayoyi game da bincike da ake na karkatar da kudaden tallafi da gwamnatin Ayodele Fayose ta yi.
Wilson Uwajaren, ya ce jami'an da aka kama sun hada da kwamishinan kudi da babban akantan jihar.
Kamen ya zo ne a ranar da gwamna Ayodele Fayose na jihar, ya bayyana kudurinsa na tsayawa takarar shugaban kasar a zaben 2019 a hukumance. (Fa'iza Mustapha)