Shugaban sashen magance yaduwar cututtuka na kasar Chikwe Ihekweazu, ya fada cikin wata sanarwa da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, tuni aka aiwatar da shiri na hadin gwiwa tsakanin hukumomi daban-daban da abin ya shafa da nufin tabbatar da ganin an shawo kan yaduwar cutar.
Daukar wannan mataki, ya biyo bayan samun rahoton bullar cutar ne da aka samu a jihar Kwara dake shiyyar arewa ta tsakiyar Najeriya, in ji mista Ihekweazu.
Ita dai cutar shawara, wasu nau'in kwayoyin cututtuka ne ke haddasa ta wadanda ake daukarsu a sanadiyyar cizon sauro.
A cewar jami'in, bisa ga ka'idar hukumar lafiya ta duniya, za'a fara gudanar da allurar riga-kafin cutar ne a yankunan da lamarin ya faru da kewayensa daga ranar 30 ga watan nan na Satumba domin dakile yaduwar cutar.
Rigakafi shi ne mataki mafi dacewa da za'a dauka domin magance bazuwar cutar shawarar.
Ita dai cutar shawara, ta kasance daya daga cikin nau'in cututtukan da ake yi wa kananan yara riga-kafin kamuwa da su a Najeriya. (Ahmad Fagam)