Ministar kudin Najeriya Kermi Adeosun wadda ta bayyana hakan yayin da take jawabi a taron kasa da kasa na yini biyu game da biyan haraji a Afirka, wanda ya gudana a Abuja, fadar mulkin kasar, ta ce babu wata kasa mai wadata da take da tsarin biyan haraji mai rauni, haka kuma babu matalauciyar kasa mai nagartaccen tsarin biyan haraji. A don haka, akwai bukatar a bullo da tsarin biyan haraji mai inganci wanda zai tabbatar da cewa, kudade haraji na shiga lalitar gwamnati yadda ya kamata.
Bugu da kari, ministar ta ce akwai bukatar bangaren majalisa da na shari'a a nahiyar su ba goyan bayan don ganin an hukunta masu kin biyan haraji. Tana mai cewa, yanzu Najeriya ce kurar baya a duniya, inda bangaren harajinta ke tallafawa GDPn kasar da kaso 6 cikin 100 kawai.
An shirya taron ne da nufin inganta matakan biyan haraji a nahiyar Afirka, ta hanyar musayar bayanai, ilimantar da jama'a, samar da horo, bayar da gudummawa ga ajandar biyan haraji a shiyyar da ma duniya baki daya. (Ibrahim Yaya)