in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cafke wani kwamandan Boko Haram a Nijeriya
2017-09-27 09:00:00 cri
Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da cafke wani kwamandan kungiyar 'yan tada kayar baya ta Boko Haram.

Kakakin rundunar Sani Kukasheka Usman ya shaidawa manema labarai a jiya cewa, 'yan sanda ne suka kama mutumin mai suna Idris Ibrahim Babawo ranar Litinin a jihar Ondo dake kudu maso yammacin kasar, inda kuma nan take suka mika shi zuwa ga rundunar sojin.

A cewar rundunar sojin, Idris Babawo shi ne mai lamba ta 156 a jerin sunayen 'ya'yan kungiyar da ta ayyana nemansu ruwa a jallo.

Sakamakon binciken farko-farko ya bayyana cewa, wanda ake zargin mai shekaru 42 ya tsere daga yankin arewa maso gabashin kasar ne saboda takurawar sojoji. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China