Pippa Malmgren, shugaba kuma wanda ya kirkiri shirin DRPM Group, ya bayyana cewa, a baya kasar Sin ta sha fama da matsalolin tattalin arziki, amma a halin yanzu matsalar ta zama tarihi, kuma shawarar "ziri daya da hanya daya" ta yi matukar taimakawa kasar wajen yin rigakafin hana fuskantar rikicin tattalin arziki.
Shawarar ta "ziri daya da hanya daya" ya taimakawa kasar Sin wajen gina alaka tsakaninta da sauran sassa na duniya, kuma hakan ya taimaka mata wajen bunkasa tattalin arzikinta na GDP na kasashen waje ta hanyar kara adadin kayayyakin da kasar ke fitarwa zuwa ketare da kuma zuba jari a kasashen waje, in ji Malmgren, wanda ya taba zama mashawarci na musamman ga tsohon shugaban Amurka George W. Bush, kan tsara tattalin ariki da hada hadar kudade.
Malmgren, ya bayyana cewa yana da muhimmanci a lura da ingancin alamu na yau da kullum wanda ke nuni da alamun karuwar adadin alkaluman tattalin arziki kamar su GDP da CPI. (Ibrahim Yaya)