Jami'in ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi yayin wata lifayar cin abinci da aka shirya don murnar bikin cika shekaru 68 da kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin wanda ta fado a ranar 1 ga watan Oktoba.
Da yake karin haske game da ci gaban alakar kasashen biyu, Chao Xiaolinag ya ce kasashen Sin da Najeriya suna da tarin albarkatun da za su kara yaukaka alakar su a fannoni daban-daban.
Ya ce, a 'yan shekarun nan, kasashen biyu sun samu tarin nasarori da ci gaba biyo bayan namijin kokarin da suka yi.
A nasa jawabin kakakin majalisar dokokin jihar Lagos, Mudashiru Ajayi Obasa, ya yaba nasarorin da kasar Sin ta samu karkashin shirinta na raya kasa. Ya ce Najeriya tana fatan yin koyi da nasarorin da kasar ta Sin ta samu tare da zurfafa hadin gwiwar tattaunawa tsakanin kasashen biyu. (Ibrahim)