Babban daraktan hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA Mustapha Maihaja, ya bayyana a garin Gombi cewa, wannan na daya daga cikin yunkurin gwamnatin kasar na bada tallafin abinci ga al'ummomin da rikicin Boko Haram ya shafa.
Maihaja ya ce, manufar bada tallafin shine, domin rage radadin ga jama'ar dake rayuwa a sansanin 'yan gudun hijirar, ya ce a wannan karo za'a bada tallafin ne ga iyalai sama da dubu 40, daga yankunan 7 wadanda rikicin ya daidaita a jahar.
Kayan da aka raba sun hada da buhhunan waken soya, gero, masara, flour, da kuma buhhunan semovita biyu dana masavita wanda aka yi kiyasin zasu iya amfani da kayan har tsawon wata guda.(Ahmad Fagam)