Al-Falih ya kara da cewa, ma'aikatar sa za ta fadada ayyukan ta na samar da cikakkiyar damar cin gajiyar albarkatun mai a cikin gida. Daga nan sai ya bayyana wasu daga karin gajiya da yake fatan kasar ta Saudiyya za ta ci daga ayyukan ma'aikatar, ciki hadda fadada masana'antu, da inganta tattalin arziki, da samar da ayyukan yi ga 'yan kasar, tare kuma da kara maida hankali ga cin gajiya daga makamashi mai tsafta.
An nada Al-Falih sabon ministan ma'aikatar makamashin kasar ne a ranar Asabar, biyowa bayan wani garambawul da aka yiwa majalissar ministocin kasar, a kuma wani mataki na tabbatar da nasarar muradun kasar na shekarar 2030. Ya kuma maye gurbin Ali Al Nuaimi, wanda ya rike ragamar ma'aikatar tsawon shekaru 21. (Saminu)