in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin kunar bakin wake ya hallaka mutane da dama a Najeriya
2017-09-19 08:57:11 cri
Sama da mutane 12 ne harin kunar bakin wake na ranar Litinin yayi sanadiyyar mutuwarsu a jahar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, kamar yadda hukumomin yankin suka tabbatar da faruwar lamarin.

An hakikance mutane sama da 26 ne suka jikkata a lokacin da wasu 'yan kunar bakin wake 3 suka tada boma bomai dake jikinsu a kauyen Mashimari dake karamar hukumar Konduga a jahar Borno, wanda keda tazarar kilomita 35 daga Maiduguri babban birnin jahar Borno.

Da yake tabbatar da afkuwar lamarin shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jahar Borno Ahmed Satomi, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an tabbatar da samun gawarwakin mutane 12 a wajen da lamarin ya faru.

Wani jami'in ya kara da cewa, suna cigaba da binciko karin gawarwaki.

Kawo yanzu babu wata kungiya data yi ikirarin daukar alhakin harin, amma an sha zargin kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram da kaddamar da munanan hare hare.

Konduga na daya daga cikin garuruwan da kungiyar Boko Haram ta karbe ikonsu a shekarar 2013. Inda daga bisani dakarun sojin kasar suka kwato garin a shekarar 2015.

Hare haren Boko Haram yayi sanadiyyar hallakar rayukan mutane sama da dubu 20, kana wasu mutanen sama da miliyan biyu suka rasa matsugunansu tun daga shekarar 2009.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China