Cikin wata sanarwar da ta fitar a jiya Jumma'a, kakakin ma'aikatar harkokin tsaron Nijeriya Manjo Janar John Enenche, ya ce bayan nazarin kwararru da abubuwan da suka faru a baya bayan nan, ya zama tilas a bayyanawa al'umma cewa, ikirarin da masu fafutukar ke yi na cewa kungiyarsu ba ta rikici ba ce, karya ne.
Sanarwar ta ce wasu daga cikin ayyukan kungiyar sun hada da kafa hukumar liken asiri ta Biafra da ikirarin kafa dakarun kasar Biafra da kuma toshe wasu hanyoyin jama'a da karbar kudi daga mutanen da ba su ji, ba su gani ba a haramtattun shingayen bincike.
Sauran sun hada da mallaka da amfani da makamai ciki har da duwatsu da adduna da fasassun kwalabe a kan soji dake sintiri a ranar 10 ga wannan watan.
Manjo Janar Enenche ya kara da cewa, kungiyar ta kuma yi fito na fito da sojoji a wani shingen bincike a ranar 11 ga watan nan, inda kuma suka yi yunkurin kwace bindigoginsu.
Rundunar tsaron Nijeriya dai na mai tabbatarwa al'ummar kasar cewa, bisa kuduri zuwa shiri da manufarta kamar yadda aka nazarta, kungiyar IPOB ta tsagerun 'yan ta'adda ce. (Fa'iza Mustapha)