Cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai, shugaban Najeriyar ya bayyana maharan a matsayin mugaye kana shedanu, sannan ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda wasu ke kokarin tayar da hankali bayan samun zaman lafiya a jihar.
A don haka ya yi kira ga masu ruwa da tsaki, da kada su bar wannan lamarin ya mayar da hannu agogo baya kan irin ci gaban da aka samu ya zuwa wannan lokaci ba. Shugaban ya kuma umarci hukumomin tsaro da su damke wadanda suka aika kashe-kashen na jihar Filato da kuma wadanda ke mara musu baya.
A ranar Jumma'ar da ta gabata ce, kwamishinan 'yan sanda na jihar Peter Ogunyanwo ya tabbatarwa manema labarai a garin Jos, babban birnin jihar kisan mutane 19, kana wasu biyar kuma suka jikkata, sakamakon wani hari da aka kai a kauyen Ancha dake karamar hukumar Bassa.
Sai dai ya ce binciken farko ya nuna cewa, wasu 'yan bindiga ne da ba a san ko su wane ne ba suka kaddamar da harin. (Ibrahim Yaya)