A wannan rana, kungiyar sa ido game da kare hakkin al'ummar Sham, wadda hedkwata a birnin London na kasar Britaniya ta ce, garin Maskanah shi ne sansanin karshe na kungiyar IS dake lardin Aleppo.
Bayan da dakarun gwamnatin Sham ta kwace birnin Aleppo, fadar lardin Aleppo a watan Disambar bara, dakarun gwamnatin sun kuma kwace yankunan masu tarin yawa a gabashin lardin sakamakon matakan sojan da suka aiwatar da nufin farautar kungiyar ta IS a lardin.
A 'yan watannin baya, dakarun sojan Sham sun sha daukar matakan soja da nufin kawar da sansanonin kungiyar IS dake cikin kasar. A yayin da dakarun gwamnatin take farautar kungiyar IS, ita kuma kungiyar sojojin sa-kai dake fafutukar wanzar da dimokuradiyya ta Sham wadda ke karkashin jagorancin Kurdawa ita ma tana kokarin yiwa garin Rakka wato hedkwatar kungiyar IS a kasar Sham kawanya. (Sanusi Chen)